Barca ta gabatar da Coutinho ga magoya bayanta

Coutinho Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Coutinho ya amince da yarjejeniya da Barcelona har zuwa 2023.

Barcelona ta gabatar da Philippe Coutinho a gaban magoya bayanta a Camp Nou a yau ranar Litinin, bayan ya saka hannu kan yarjejeniya da kungiyar.

Dan wasan Brazil, mai shekara 25 ya koma Spaniya da murza-leda kan kudi da ake tunanin sun kai fam miliyan 160, bayan da Liverpool ta amince da cinikin a ranar Asabar.

Dan wasan ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara biyar da rabi a gaban shugaban Barcelona Josep Maria Bartomeu.

Kuma duk kungiyar da take son daukarsa sai ta biya fam miliyan 355 idan kwantiraginsa bai kare a Barca ba.

Coutinho ya dauki hoto a Camp Nou da wasu 'yan wasa da jami'ai, bayan da Barcelona ta doke Levante 3-0 a gasar La Liga a ranar Lahadi.

Barcelona ta gabatar da Coutinho ga magoya bayanta da misalin karfe 11:30 agogon GMT a yau Litinin a Camp Nou.

Labarai masu alaka