Real da Celta sun raba maki a tsakaninsu

La Liga Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Real Madrid tana nan a matakinta na hudu a kan teburin La Liga da maki 32

Real Madrid ta tashi wasa 2-2 da Celta Vigo a gasar La Liga karawar mako na 18 da suka yi a ranar Lahadi.

Celta wadda ta karbi bakuncin Real ce ta fara cin kwallo ta hannun Daniel Wass a minti na 33 da fara tamaula, kuma minti biyu tsakani Gareth Bale ya farke wa Real Madrid.

Bale ne dai ya ci wa Madrid kwallo na biyu biyu, yayin da Celta ta farke saura minti bakwai a tashi daga fafatawar.

Da wannan sakamakon Real Madrid tana nan a matakinta na hudu a kan teburin La Liga da maki 32 da kwantan wasa daya.