Messi ya ci kwallo a wasansa na 400 a Barcelona

Barcelona Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Messi ya ci kwallo 16 a gasar La Liga ta kakar bana

Lionel Messi ya ci kwallo a wasa na 400 da ya buga wa Barcelona a karawar da ta doke Levante 3-0 a gasar cin kofin La Liga a ranar Lahadi.

Messi ne ya fara cin kwallo kuma na 365 da ya zura a raga jumulla, wanda hakan ya sa ya yi kan-kan-kan da Gerd Muller a yawan cin kwallaye a gasar manyan kasashen Turai.

Messi dan kwallon tawagar Argentina ya zura kwallo 16 a gasar La Liga ta shekarar nan.

Kwallo daya Messi ke bukata domin ya haura tarihin yawan cin kwallaye da Muller ya kafa a gasar Bundesliga a kungiyar Bayern Munich tsakanin 1964 zuwa 1979.

Barcelona tana nan a matakinta na daya a kan teburin La Liga.

Labarai masu alaka