Arsenal da City na zawarcin Jonny Evans

West Brom Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Alan Pardew ya ce za su gabatar wa da Evans kwantiragi mai tsoka domin ya ci gaba da zama a West Brom

Arsenal da Manchester City sun tuntubi West Brom ko za a sayar musu da Jonny Evans.

Kocin Arsenal, Arsene Wenger zai nemi mahukuntan kungiyar su sayi dan wasan mai tsaron baya kan fam miliyan 25.

Arsenal ta kuma san da cewar West Brom ta dade tana son sayen Mathiieu Debuchy wanda ke son buga tamaula akai-akai.

Manchester City tana son sayen dan kwallon da zai maye gurbin Vincent Company, wanda yake jinya, duk da Eliaquim Mangala na buga gurbinsa.

Evans ya koma West Brom daga Manchester United kan fam miliyan 6 a Agustan 2015.

A lokacin bazara West Brom ba ta sallama tayin da Arsenal da Manchester City da Leicester City suka yi dan wasan ba.

Labarai masu alaka