Liverpool ta ci riba a cinikin Coutinho

Liverpool Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Coutinho ya saka hannu a Barca a ranar Litinin a Camp Nou

Liverpool ta ci ribar fam miliyan 134 a cinikin Philippe Coutinho da ta sayar wa Barcelona.

Coutinho dan kwallon Brazil, ya koma Anfield da murza-leda daga Milan a shekarar 2013 kan kudi fam miliyan takwas.

Sai dai ranar Asabar Liverpool ta amince da tayin Barcelona a kan Coutinho na fam miliyan 142.

Tuni dan wasan ya sa hannu kan yarjejeniya a Barcelona ranar Litinin, inda kungiyar ta gabatar da shi a gaban magoya bayanta.

Sai dai kuma dan kwallon na yin jinya, inda ake sa ran zai fara buga Barcelona tamaula a watan Fabrairu.

Coutinho ya buga wa Liverpool wasan Firimiya 152, inda ya ci kwallo 41 ya kuma taimaka aka ci 31.