Wydad Casablanca ta kori Hussein Amotta

Wydad Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Amotta ya ja ragamar Wydad shekara daya

Wydad Casablanca mai rike da kofin Zakarun nahiyar Afirka ta sallami kocinta Hussein Amotta, bayan da kungiyar ba ta taka rawar gani a bana.

Amotta wanda ya lashe kofin gasar Morocco a 2017, yana daga cikin wadanda suka yi takarar gwarzon koci da babu kamarsa a Afirka a 2017.

Kocin Masar, Hector Cuper ne ya lashe kyautar da hukumar kwallon kafa ta Afirka, Caf ta gudanar a watan Janairu a Accra, Ghana, ciki har da Gernot Rohr na Nigeria.

Wydad ta gabatar da taro a ranar Talata inda ta fitar da sanarwar korar kocin tare da mataimakansa, kan kasa taka rawar gani a bana.

Amotta ya karbi aikin horar da Wydad a watan Janairun 2017, inda ya maye gurbin Sebestian Desabre wanda ya koma kungiyar Ismaili, yanzu shi ne kocin tawagar Uganda.

Wydad mai rike da kofin gasar Morocco mai kungiyoyi 16 tana ta 12 a kan teburi da tazarar maki 13 tsakaninta da Hassania Agadir wadda ke matsayi na daya.

Labarai masu alaka