'Yan Madrid 19 da za su kara da Numancia

Copa del Rey Hakkin mallakar hoto Real Madrid
Image caption Madrid tana ta hudu a kan teburin La Liga da maki 32

Zinedine Zidane ya bayyana 'yan wasa 19 da za su buga wa Real Madrid gasar Copa del Rey da Numancia a ranar Laraba a Santiago Bernabeu..

A wasan farko da suka kara a gasar, Real Madrid ce ta doke Numancia 3-0.

'Yan wasan Madrid 19 da za su fuskanci Numancia:

Masu tsaron raga: Navas da Casilla da kuma Moha.

Masu tsaron baya: Carvajal da Vallejo da Nacho da Theo da Achraf da kuma Tejero.

Masu wasan tsakiya: Kroos da Casemiro da Llorente da Asensio da Isco da Kovacic da Ceballos da kuma Oscar.

Masu cin kwallo: Vazquez da kuma Mayoral.

Labarai masu alaka