Wane zumunci ne tsakanin Barcelona da Liverpool?

Barcelona Hakkin mallakar hoto Barcelona
Image caption Barcelona tana mataki na daya a kan teburin La Liga

Philippe Coutinho shi ne dan wasan Brazil na 33 da ya koma Barcelona a tarihi, bayan da dan wasan ya bar Anfield a ranar Asabar.

A ranar Litinin Barcelona ta kaddamar da shi a gabayn magoya bayanta a Camp Nou, bayan da ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyar da rabi kan fam miliyan 142.

Haka kuma Coutinho shi ne dan wasa na takwas da ya buga wa Liverppol tamaula sannan ya koma Camp Nou da taka-leda.

'Yan wasa biyu da yanzu haka ke buga wa Barcelona wasa da suka je kungiyar daga Liverpool sun hada da Javier Mascherano da ya koma a 2010 da Luis Suarez da ya je a 2014.

Wasu 'yan kwallon sun koma barcelona kai tsaye daga Liverpool, wasu kuwa sai da suka buga wata kungiyar kafin su koma Camp Nou, amma sun yi wasa a Anfield.

Ga jerin 'yan wasan da suka buga Liverppol sannan suka koma Barcelona:

  • Mauricio Pellegrino Sai da ya yi shawagi
  • Boudewijn Zenden Sai da ya yi shawagi
  • Jari Litmanen Kai tsaye ya koma Barca daga Liverpool
  • Pepe Reina Kai tsaye ya koma Barca daga Liverpool
  • Luis García Kai tsaye ya koma Barca daga Liverpool
  • Javier Mascherano Kai tsaye ya koma Barca daga Liverpool
  • Luis Suárez Kai tsaye ya koma Barca daga Liverpool

Labarai masu alaka