Lukaku zai dauki matakin shari'a kan Everton

Everton Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Lukaku ya koma Old Trafford kan fam miliyan 75

Dan wasan Manchester United, Romelu Lukaku ya ce zai dauki matakin shari'a kan kalaman da shugaban Everton, Farhad Moshiri ya yi kan dan kwallon.

Moshiri ya ce Lukaku ya yanke shawarar barin Everton ne bayan da ya samu wani sako daga matsafa.

Lukaku ya koma Old Trafford da taka-leda kan fam miliyan 75 a watan Yuni, bayan da bai amince da tayin tsawaita zamansa a Everton ba.

Wakilan Lukaku sun shaidawa BBC cewar, shawarar da Lukaku ya yanke ta koma wa United ba ta shafi sakon matsafan ba.

Sashin wasanni na BBC ya fahimci cewar dan kwallon ya bar kungiyar da fuci da kuma bacin ran zargin.

Labarai masu alaka