Ingila za ta yi wasan sada zumunta da Nigeria

England Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ingila tana rukuni na bakwai a gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018

Tawagar kwallon kafa ta Ingila za ta buga wasan sada zumunta da ta Nigeria a shirin da take yi na fafatawa a gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha.

Ingila na fatan yin wasa da Super Eagles a Wembley a ranar 2 ga watan Yuni.

Haka kuma tawagar ta Ingila za ta yi wasan sada zumunta da Costa Rica a Elland Road ranar 7 ga watan Yuni, sannan ta wuce zuwa Rasha.

Ingila wadda Gareth Southgate ke horar wa tana rukuni na bakwai da ya kunshi Tunisia da Panama da kuma Belgium.

Nigeria kuwa tana rukuni na hudu da ke dauke da Argentina da Iceland da kuma Croatia.