Barcelona ta dauki Yerry Mina

Barcelona Hakkin mallakar hoto Barcelona
Image caption Baracelona tana mataki na daya a kan teburin La Liga

Barcelona ta sanar da daukar mai tsaron baya, Yerry Mina daga Palmeiras kan kudi fam miliyan 11 da dubu 800.

Dan wasan dan kasar Colombia ya amince da yarjejeniyar sheka biyar domin murza-leda a Camp Nou.

Barcelona ta gindaya fam miliyan 100 ga duk kungiyar da za ta dauki dan wasan idan har yarjejeniyarsa ba ta kare ba.

Nan gaba Barcelona za ta sanar da ranar da Mina zai saka hannu kan kwantiragi da gabatar da shi a gaban magoya bayanta.

Labarai masu alaka