Ko Bernabeu ya zama damisar takarda ne?

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Real Madrid tana ta hudu a kan teburin La Liga

Real Madrid ta kai wasan zagayen gaba a Copa del Rey, duk da tashi 2-2 da ta yi da Numancia a karawar da suka yi a Santiago Bernabeu a ranar Laraba.

A baya can filin wasa na Real Madrid kan jefa fargaba ga duk kungiyar da za ta je wasa a ciki, domin sai ta sha kashi, idan ba ta yi sa'a ba da kwallaye da yawa.

Sai dai filin na Bernabeu a kakar bana ya daina ba wa kungiyoyi tsoron karawa a cikinsa, inda Real ta sha kashi a wasa biyu da canjaras biyar a bana.

Cikin kungiyoyin da suka ci Madrid a Bernabeu a kakar bana sun hada da Barcelona da kuma Real Betis.

Wadanda suka yi canjaras a gidan Madrid sun hada da Valencia da Levante da Tottenham da Fuenlabrada da kuma Numancia.

Haka kuma an zura wa Real kwallo 16 a gida bana, yayin da a kakar 2016/17 kwallo 30 ne ya shiga ragarta a gasar gaba daya.

Labarai masu alaka