Leipzig ba za ta bar Keita ya koma Liverpool ba

Liverpool Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Liverpool tana ta hudu a kan teburin Premier da maki 44

Kungiyar RB Leipzig ta shaida wa BBC cewar ba ta da niyyar barin Liverpool ta kammala daukar Naby Keita a Janairun nan.

A watan Agustan 2017, Liverpool ta amince ta biya fam miliyan 51 kudin daukar Keita, domin ya koma wasa a Anfield idan an kammala gasar bana.

Wasu rahotanni sun ce Leipzig za ta iya karbar karin kudi da ya kai fam miliyan 15, idan har Liverpool na son dan kwallon Guinea ya koma can da murza-leda.

Leipzig ta ce Liverpool ba ta tuntube ta ba, kuma babu wata maganar cewar Keita zai koma Anfield da taka-leda a Janairun nan.

Liverpool ta sayar wa da Barcelona Philippe Coutinho kan fam miliyan 142 a ranar Asabar, inda ya saka hannu kan yarjejeniya a ranar Litinin a Camp Nou.

Labarai masu alaka