Dan wasan Arsenal Walcott 'zai koma' Everton

Walcott has scored 108 goals for Arsenal since joining in 2006 Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Walcott ya ci wa Arsenal kwallo 108 tunda ya koma kulob din a 2006

Kocin Everton Sam Allardyce cya tabbatar da cewa kulob din na tattaunawa da Arsenal da zummar sayen Theo Walcott a kan kwantaragi na dindindin.

Allardyce ya ce dan wasan mai shekara 28 zai kara wa kulob din tagomashi sannan ya rika zura kwallo.

Ya kara da cewa: "Ina tsammanin babu yiwuwar mu karbi aronsa. Ba mu cimman matsaya ba amma dai muna ci gaba da tattaunawa.

"Zan yi matukar farin ciki idan wani dan wasa, ko da ba Thoe ba ne, ya dawo kulob dinnan."

Allardyce, wanda ya sayi Cenk Tosun daga Besitkas a kan £27 a watan Janairu, ya ce ba zai sake sayen wani dan wasa ba bayan ya sayi Walcott sai dai idan dan wasan kulob din ne ya bar Everton.

Ya ce Walcott dan wasa ne da aka gwada kuma aka ga kwarewarsa musamman kan yadda yake kai munanan hare-haren cin kwallo da kuma iya bayar da kafa.

"Ya ci wa Arsenal kwallo 100 daga tazara mai nisa," in ji Allardyce. "Yana da matukar gudu ba kamar yadda muke ba. Don haka yana da matukar muhimmanci in samu mai ci min kwallo. Shekarunsa 28 kacal.

Walcott - wanda sau biyu yana daukar kofin FA da Arsenal - ya buga wasa 395 a kakar wasa 13 tunda ya koma kulob din daga Southampton a 2006 a kan £5m.

Amma wasan minti 47 kawai ya buga a gasar Premier ta bana.

Labarai masu alaka

Karin bayani

Labaran BBC

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba