Alexis Sanchez zai bar Arsenal a watan Janairun nan?

Alexis Sanchez Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Alexis Sanchez ya ci kwallo takwas cikin wasa 21 da ya yi wa Arsenal a kakar wasa ta bana

Dan wasan gaba na Arsenal Alexis Sanchez zai bar kulob din a watan nan na Janairu idan aka yi tayin da ya dace da shi sannan aka samu wanda zai maye gurbinsa.

An fahimci cewa shugabannin Arsenal sun amince Sanchez ya tafi bayan ya kwashe shekara uku da rabi yana yi wa kulob din wasa.

Amma Arsenal na jan kafa wurin sayar da shi ba tare da samun dan wasan da zai maye gurbinsa ba kuma yanzu haka suna son sayen dan wasan Bordeaux mai shekara 20 Malcom.

"A al'adance ya kamata a zauna a nan zuwa karshen kakar wasa ta bana, amma dai za mu ga abin da zai faru," in ji kocin Arsenal, Arsene Wenger.

Da yake magana da manema labarai ranar Juma'a, Wenger ya kara da cewa: "Har yanzu babu wani tartibin abu kuma ba a cimma matsaya kan batunsa ba. Amma ina so a cimma matsaya cikin gaggawa."

Ana sa ran dan wasan mai shekara 29 zai koma Manchester City kuma an ce kulob din biyu sun tattauna a kansa amma ba su cimma matsaya kan kudin sayensa ba."

Rahotanni na cewa Arsenal na son sayar da shi a kan £35m, amma City sun ce za su biya £20m.

Majiyoyi sun ce watakila kulob-kulob din za su cimma matsaya a kan tsakanin £25m da £30m.

Labarai masu alaka