Giggs ya zama kocin Wales

Ryan Giggs ya taba zama kocin-riko a Manchester Unitedinda ya jagoranci buga wasa hudu a 2014 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ryan Giggs ya taba zama kocin-riko a Manchester Unitedinda ya jagoranci buga wasa hudu a 2014

Hukumar kwallon kafa ta Wales ta sanar da Ryan Giggs a matsayin kocin tawagar kasar.Hukumar ta kira taron 'yan jarida a ranar Litinin domin bayyana Giggs wanda zai maye gurbin Chris Coleman.Tsohon dan wasan na Manchester United ya saka hannu kan kwantiragin shekara hudu.Chris Coleman ya bar aikin horar da tawagar Wales a watan Nuwamba inda ya koma jan ragamar Kungiyar Sunderland.Cikin wadanda hukumar Wales ta tattauna da su kan bai wa aikin horar da tawagar kasar har da Craig Bellamy, da Osian Roberts da kuna Mark Brown.

Labarai masu alaka