Liverpool ta taka wa Man City burki

Sadio Mane Hakkin mallakar hoto Getty Images

Liverpool ta taka wa Manchester City burki bayan da ta yi wasanni 22 ba tare da yin rashin nasara ba a Gasar Premier.

Liverpool ta doke City ne da ci 4-3 a Anfield ranar Lahadi.

Kodayake, Man City za ta ci gaba da kasance a saman teburin gasar da bambancin maki 15, yayin da Liverpool ta koma tamaki na uku.

Wannan ne wasa na farko da Liverpool ta yi tun bayar sayar da Philippe Coutinho ga Barcelona.

Hakazalika ita ma Arsenal ta yi rashin nasar a hannun Bournemouth da ci 2-1.

Karanta wadansu karin labarai

Labarai masu alaka