Plateau ta fara Firimiya da kafar dama

Karon farko da Plateau United ta ci kofin Firimiyar Nigeria, Mighty Jets ta taba dauka a 1972 Hakkin mallakar hoto LMCNPFL
Image caption 2017 ne karon farko da Plateau United ta ci kofin Firimiyar Nigeria, Mighty Jets ta taba dauka a 1972

Mai rike da kofin gasar kwallon kafar Firimiyar Nigeria, Plateau United ta fara wasannin bana da kafar dama.A wasannin makon farko da aka yi a karshen mako ne Plateau United ta je gidan Nasarawa United ta ci ta daya mai ban haushi a ranar Lahadi.Raphael Ayagu ne ya ci wa Plateau United kwallon saura minti uku a tashi daga karawar.Tun a ranar Asabar aka fara gasar Firimiyar Nigeria ta bana inda Katsina United da Kano Pillars suka tashi 2-2.Cikin wasa 10 da aka yi kungiyoyi biyu ne suka ci wasa a waje, haka kuma wadanda suka buga wasan su a waje sun ci kwallo bakwai a raga.Wannan sakamakon daidai yake da wasan farko a gasar bara.Ga sakamakon wasannin makon farko:Kwara 0-2 TornadoesFCIU 2-1 Yobe StarsWikki 1-0 Go RoundAkwa 2-0 RangersLobi 1-1 EnyimbaHeartland 0-0 SunshineNasarawa 0-1 PlateauRivers 1-0 El-KanemiAbia Warriors 2-0 MFMKatsina 2-2 Pillars

Labarai masu alaka