Manchester City ta fasa sayen Alexis Sanchez

Alexis Sanchez Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Arsenal ta sayi Alexis Sanchez a shekarar 2014 a kan £31.7

Manchester City ta yanke shawarar kin sayen dan wasan gaba na Arsenal Alexis Sanchez.

Kungiyar ta dauki wannan matakin ne saboda, a cewarta dan wasan mai shekara 29 yana da matukar tsada.

Kocin City Pep Guardiola, da masu kungiyar Khaldoon al Mubarak da sauran manyan jami'anta duk sun amince kada a sayi dan wasan.

An fahimci cewa kudin da aka ce City ta bayar domin sayen Sanchez ya zarta wanda ta sayi dukkan manyan 'yan wasanta, abin da ya sa kungiyar ta fasa sayensa.

Ana sa ran Manchester United za ta sayi dan kasar ta Chile bayan sun nuna cewa za su saye shi kan farashin da aka sanya, wato £35m.

Majiyoyin da ke da masaniya kan batun sun ce Chelsea ma tana da sha'awar sayen dan wasan.

Labarai masu alaka