Babu batun komawar Mkhitaryan Arsenal

Man United Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mkhitaryan ya yi wasa 22 a Manchester United a bana

Ba a kulla yarjejeniyar da ta kunshi musaya cewar Henrikh Mkhitaryan na Manchester United zai koma Arsenal, ita kuma ta bayar da Alexis Sanchez ba.

Wata majiya ce ta kusa da Mkhtaryan ta shaida wa BBC cewar babu wata yarjejeniya da dan kwallon ya amince da ita kawo yanzu ta koma wa Arsenal da taka-leda.

Sai dai kuma rahotanni na cewar Sanchez ya amince da kwantiragin da Manchester United ta yi masa tayin koma wa Old Trafford da murza-leda a Janairun nan.

Sai dai kuma watakila Sanchez zai koma United ne da amincewar Mkhitaryan zai koma Gunners da taka-leda.

Wata majiyar ta ce Chelsea ma tana son daukar Mkhitaryan dan wasan tawagar Armenia.

A watan Yunin 2016 United ta sayi Mkhitaryan daga Burussia Dortmund kan fam miliyan 26, a lokacin da Arsenal ta dade tana zawarcin dan kwallon.

A karshen kakar bana ne kwantiragin Sanchez zai kare a Arsenal.

Labarai masu alaka