Mourinho zai ci gaba da zama a Old Trafford

Manchester United Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mourinho ya koma United ne a watan Mayun 2016

Manchester United ta kusa cimma kulla yarjejeniya da Jose Mourinho kan tsawaita zamansa a Old Trafford.

Tuni tattaunawar ta yi nisa, illa lokaci ake jira da Mourinho zai saka hannu kan sabon kwantiragin da zai ci gaba da horar da United tamaula, bayan da yarjejeniyarsa zai cika a 2019.

Mourinho ya koma United a watan Mayun 2016, inda ya lashe League Cup da na Europa a kakar farko da ya ja ragamar kungiyar.

Sai dai kuma a wata tattaunawa da Mourinho ya yi a farkon watan Janairu da 'yan jarida ya ce batun babu kanshin gaskiya a ciki.

Kocin baya farinci kan yadda United ba ta fitar da kudi ya kara sayo 'yan wasa ba, saboda haka bai bar otal din da yake zaune ba, inda aka ce yana shirin barin kungiyar ne.

Hakan ne ya sa ake cewa United ta amince ta sayi Alexis Sanchez na Arsenal.

Labarai masu alaka