Ronaldo da Madrid jini da tsoka ne — Zidane

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kwallo hudu kacal Ronaldo ya ci wa Real a gasar La Liga a bana

Zinadine Zidane ya ce bai san yadda Real Madrid za ta tsinci kanta idan Cristaino Ronaldo baya buga wa kungiyar tamaula ba.

Wasu rahotannio na cewa Ronaldo dan kwallon tawagar Portugal na son barin Madrid kan takaddamar kwantiraginsa da shugaban Real, Florentino Perez, kuma Manchester United zai koma.

Dan wasan yana da yarjejeniya a Bernabeu zuwa 2021, kuma Zidane ya yi kira da cewar ya kamata dan wasan ya mai da hankalinsa kan buga wa kungiyar tamaula.

Zidane ya ce Ronaldo yana kokari a Madrid, kuma shi ne kashin bayan kungiyar, domin yana bayar da gagarumar gudunmawa.

Kocin ya ce baya son yin magana kan kwantiragin dan kwallon, shi dai ya san cewar Real ta Ronaldo ce domin sun da ce.

Madrid tana ta hudu a kan teburin La Liga, bayan da Villarel ta doke ta 1-0 a ranar Asabar a Bernabeu, kuma kwallo hudu kacal Ronaldo ya ci a gasar La Liga ta bana.

Labarai masu alaka