Plateau ta hada maki shida a wasa biyu a Firimiya

Nigerian Premier League Hakkin mallakar hoto NPFL Twitter
Image caption Plateau United ta hada maki shida a wasa biyu da ta buga a gasar Premier ta bana

Mai rike da kofin Premier Nigeria, Plateau United ta hada maki uku, bayan da ta ci Rivers United 2-0 a wasan mako na biyu da suka kara a ranar Laraba.

Plateu United ta fara cin kwallo ta hannun kyaftin dinta Elisha Golbe a bugun tazara, sannan ta ci na biyu ta hannun Emeka Umeh.

Plateu United wadda ta ci Nasarawa United daya mai ban haushi a ranar Lahadi, ta hada maki shida kenan a wasa biyu da ta buga.

Ita ma kuwa Kano Pillars 2-0 ta doke Nasarawa United, inda Junior Lokosa ya ci kwallo ta hannun Junior Lokosa da kuma Alassan Ibrahim.

Ga sakamakon wasannin mako na biyu da aka buga:

  • MFM 1-0 Kwara
  • Yobe Stars 2-0 Wikki
  • Rangers 1-2 Lobi
  • El-Kanemi 1-0 Abia Warriors
  • Sunshine 2-1 Katsina
  • Go Round 1-0 Akwa
  • Tornadoes 2-1 FCIU
  • Enyimba 0-0 Heartland

Labarai masu alaka