An sace Amurkawa a Kaduna

Donald Trump Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An sace Amurkawa biyu da 'yan Canada biyu a Kaduna

Rundunar 'yan sandan Jihar Kaduna a Najeriya ta tabbatar da sace wasu turawa guda hudu da suka kunshi Amurkawa guda biyu da 'yan kasar Canada guda biyu.

Rundunar 'yan sandan jihar kuma ta ce an kashe 'yan sandan Najeriya guda biyu da ke ba turawan kariya a Kaduna.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna wanda ya tabbatar da sace turawan, ya shaidawa BBC cewa 'yan bindigar sun sace su ne kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Sannan ya ce rundunar 'Yan sandan jihar tana iya kokarinta domin kubutar da turawan a raye wadanda ke aiki a yankin Kafanchan.

Babu dai wani cikakken bayani game da Turawan da kuma yadda 'yan bindigar suka yi awon gaba da su.

Satar mutane don neman kudin fansa na dada kamari a Najeriya, a daidai lokacin da kasar ke fama rikicin Boko Haram da matsin tattalin arziki mafi tsanani a shekaru da dama.

Kuma Jihar Kaduna na daga cikin sassan kasar da suka fi fama da sace-sacen mutane don neman kudin fansa.

Labarai masu alaka