Mkhitaryan ya amince zai koma Arsenal

Man United Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dan wasan ya ci wa United kwallo 13 a wasa 63 da ya yi

Dan wasan Manchester United, Henrikh Mkhitaryan ya amince zai koma Arsenal, cikin wata yarjejeniyar da Alexis Sanchez zai je Old Trafford da murza-leda.

Arsenal za ta duba lafiyar Mkhitaryan mai shekara 28 a ranar Lahadi da Litinin, yayin da likitocin United za su duba lafiyar Sanchez a ranar Lahadi.

Sai dai ba a fayyace kunshin kwantiragi da dan wasan zai saka hannu ba, da kuma albashin da Arsenal za ta dinga biyan shi ba.

Arsenal Hakkin mallakar hoto BBC Sport

United ta yi nasarar sayen Mkhitaryan daga Borussia Dortmund kan fam miliyan 26.3 a Yulin 2016, a lokacin da Arsenal ke zawarcin dan kwallon.

Dan wasan ya buga wa United wasa 63, inda ya buga fafatawa 22 a Premier kakar nan, ya kuma ci kwallo 13.

Shi kuwa Sanchez ya ci kwallo 80 a wasa 166 da ya yi wa Gunners a dukkan fafatawa, tun lokacin da ya koma Emirates daga Barcelona kan fam miliyan 35 a Yulin 2014.