Aubameyang zai kai fam miliyan 50 a Arsenal

Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sau biyu Borussia Dortmund na hukunta Aubameyang kan halin rashin da'a

Arsenal na bukatar fam miliyan 50 domin sayen dan kwallon Borussia Dortmund, Pierre-Emerick Aubameyang in ji wata majiya da take kusa da kungiyar.

A ranar Juma'a daraktan wasannin Dortmund, Michael Zorc ya kira Arsene Wenger da rashin girmamawa, saboda ya yi kalamai a cikin jama'a kan dan kwallon.

Wenger kocin Arsenal ya ce dan kwallon na tawagar Gabon zai da ce da salon yadda Gunners ke murza-leda.

Kungiyoyin biyu na tattauna wa domin cimma matsaya, inda Arsenal za ta biya fam miliyan 46.5 da kuma bayar da Alexandre Lacazette ga Dortmund.

Idan Aubameyang ya koma Arsenal ana sa ran zai yi wasa tare da Henrikh Mkhitaryan wanda suka murza-leda a Dortmund, yayin da Alexis Sanchez zai koma Manchester United.