Real Madrid ta casa Deportivo La Coruna

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Real Madrid mai kwantan wasa daya ta hada maki 35 kenan

Real Madrid ta doke Deportivo La Coruna da ci 7-1 a gasar La Liga wasan mako na 20 da suka kara ranar Lahadi a Santiago Bernabeu.

Deportivo ce ta fara cin Madrid ta hannun Adrian Lopez a minti na 23 da fara tamaula, yayin da Real ta farke ta hannun Nacho.

Real Madrid ta kara cin kwallo na biyu ta hannun Gareth Bale saura minti hudu a tafi hutu.

Bayan da aka dawo ne daga hutu Bale ya ci kwallo kuma na biyu a karawar sai Luka Modric ya kara na hudu sannan Ronaldo ya ci guda biyu a wasan.

Daf kuma da za tashi daga wasan Nacho ya kara cin kwallo kuma shi ma na biyu da ya ci a gumurzun.

Rabon da Cristiano Ronaldo ya ci kwallo a gasar La Liga tun biyun da ya ci Sevilla a karawar da Madrid ta yi nasara cin 5-0 a cikin watan Disamba.

Real wadda take da kwantan wasa daya ta hadi maki 35 kenan a wasa 19 da ta buga a gasar La Liga.

Labarai masu alaka