Man City ta tsawaita zaman De Bruyne a Ettihad

Man City Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption De Bruyne ya ci kwallo shida ya kuma taimaka aka ci 10 a bana

Manchester City ta tsawaita yarjejeniyar dan wasanta Kevin de Bruyne domin ya ci gaba da zama a Ettihad.

A karshen kakar 2021 ne kwantiragin De Bruyne dan wasan tawagar kwallon kafar Belgium zai kare a City.

Sai dai kuma City ta kara tsawaita zaman tsohon dan wasan Chelsea zuwa karshen kakar 2023.

Kungiyar ta yi haka ne, sakamakon rawar da yake takawa a kungiyar tun bayan da ya koma City daga Wolfsburg kan fam miliyan 55.

De Bruyne ya je Chelsea a 2012 daga Genk, sai dai wasa uku kacal ya buga, daga nan ya koma Wolfsburg a 2014.

Labarai masu alaka