Messi da Suarez sun ci kwallo 34 a La Ligar bana

Barcelona Hakkin mallakar hoto Barcelona FC
Image caption Messi da Suarez sun ci kwallo 34 a gasar La Liga ta bana

Dan wasan tawagar kwallon kafar Argentina da na Uruguay, Lionel Mesi da Luis Suarez sun ci wa Barcelona kwallo 34 a gasar La Liga ta bana.

A ranar Lahadi ne Barcelona ta doke Real Betis da ci 5-0, kuma Messi da Suarez kowannensu ya ci kwallo bibiyu a raga, jumulla Messi ya ci 19 shi kuwa Suarez yana da 15 a La Ligar bana.

Messi ya ci kwallo 25 tun fara kakar shekarar nan, inda ya ci 19 a La Liga da uku a kofin Zakarun Turai da biyu a Copa del Rey da daya a Spanish Super Cup.

Wannan kuma ita ce kaka ta goma a jere da Messi ke cin kwallo 25 ko fiye da hakan a kungiyar ta Barcelona wadda ke ta daya a kan teburin wasannin bana.

Lionel Messi ya ci kwallo biyu a wasa daya sau biyar a karawa da Alaves da Juventus da Las Palmas da Celta da kuma Betis, ya kuma ci Espanyol kwallo uku sannan ya zura wa Eiba kwallo hudu.

Shi kuwa Suarez ya ci kwallo biyu sau hudu a wasa da Leganes da Deportivo da Real Sociedad da kuma Betis.

Labarai masu alaka