CHAN: Nigeria za ta kara da Equatorial Guinea

CHAN 2018 Hakkin mallakar hoto NPFL Twitter
Image caption Nigeria tana ta daya a kan teburin rukuni na uku da maki hudu

Tawagar kwallon kafa ta Nigeria za ta kara da ta Equatorial Guinea a ranar Talata a gasar cin kofin nahiyar Afirka wato CHAN da Morocco ke karbar bakunci.

Super Eagles wadda ke ta daya a rukuni na uku da maki hudu a wasa biyu da ta yi, za ta kara da Equatorial Guinea wadda take ta karshe mara maki ko daya.

A dai ranar ta Talata ne Libya za ta fafata da Rwanda, bayan da Rwanda ke ta biyu da maki hudu, ita kuwa Libya tana ta uku a teburi na uku da maki uku.

Tawagar da ta kai wasannin zagaye na biyu sun hada da Morocco da Sudan da Zambia da kuma Namibia.

Labarai masu alaka