United ce kan gaba wajen samun kudin shiga

Man United Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Man United tana ta biyu a kan teburin Premier ta bana.

Manchester United ta ci gaba da rike matsayinta na kungiyar kwallon kafa da ta fi samun kudin shiga a duniya, in ji wani rahoto mai suna Money League da kamfanin akantoci da Deloitte ya fitar.

United ta samu fam miliyan 581 a kakar wasanni ta 2016/17, bayan da ta dara Real Madrid da fam miliyan 1.5; wannan ce tazara mafi kankanta a shekara 21 da aka yi ana fitar da bayanan.

Kuma kofin Zakarun Turai da ta lashe ne ya sa ta dara Barcelona wadda ke mataki na uku.

Bayern Munich, mai buga gasar Bundesliga, ce ta hudu sai Manchester City ta biyar wadda ta samu kudin shigar da ya kai fam miliyan 454 a bara.

Arsenal ta karbe mataki na shida, wanda Paris St Germain take kai a bara, yayin da Chelsea da Liverpool ke cikin goman farko.

Labarai masu alaka