Inter Milan ta dauki aron Rafinha

Barcelona Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rafinha ya buga wa Barcelona wasa 79 ya kuma ci kwallo 11

Inter Milan ta dauki aron Rafinha daga Barcelona, domin ya buga mata wasanni aro zuwa 30 ga watan Yunin 2018.

Inter Milan za ta iya sayen dan wasan kan Yuro miliyan 35 idan ya taka mata rawar da take so, sannan ta sanar da Barcelona idan za ta biya kudin dan kwallon kafin karshen kakar bana.

Haka kuma Inter Milan ce za ta dauki alhakin biyan albashin Rafinha kamar yadda suka cimma yarjejeniya a tsakanin kungiyoyin biyu.

Rafinha ya koma Barcelona yana da shekara 13, inda ya fara buga wa babbar kungiyar tamaula a karkashin Pep Guardiola ranar 9 ga watan Nuwambar 2011.

Dan wasan dan kasar Brazil ya ci kofi tara a Barcelona ciki har da na Zakarun Turai biyu da Copa del Rey uku da European Super Cup da Spanish Super Cup da kofin Zakarun nahiyoyin duniya.

Rafinha ya buga wa Barcelona wasa 79 ya kuma ci kwallo 11.