Morocco ta fara zawarcin gasar kofin duniya ta 2026

Morocco
Image caption Afirka ta Kudu ce tilo daga Afirka da ta taba karbar bakuncin kofin duniya

Morocco ta kaddamar da zawarcin gasar cin kofin duniya ta 2026 da bayyana butun-butumin da za ta yi amfani da shi a taron da ta gudanar a Casablanca a ranar Talata.

Wannan ne karo na biyar da Morocco ke son karbar bakuncin gasar cin kofin duniya, inda take takara da Canada da Mexico da Amurka.

Morocco wacce ke karbar bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 'yan wasan da ke taka-leda a nahiyar wato CHAN, ta yi zawarcin gasar kofin duniya a 1994 da 1998 da 2006 da kuma 2010.

A ranar 13 ga watan Yuni ne hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa za ta bayyana kasar da za ta karbi bakuncin wasannin a lokacin gasar kofin duniya a Rasha a 2018.

Kasar Afirka ta Kudu ce ta taba karbar bakuncin gasar cin Kofin duniya a 2010 a nahiyar, tun lokacin da aka fara wasannin a 1930.

Labarai masu alaka