Henry bai ce na bar Arsenal ba - Sanchez

Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sanchez ya ci wa Arsenal kwallo 80 tun komawarsa can a 2014 daga Barcelona

Sabon dan wasan Manchester United, Alexis Sanchez ya ce Thierry Henry bai ce masa ya bar Arsenal ba, don radin kansa ya yanke shawarar barin kungiyar.

Bayan da dan kwallon tawagar Chile ya koma United ne Arsenal ta karbi Henrikh Mkhitaryan, sai Sanchez ya kawo misalin tattaunawar da ya taba yi da Henry.

A ranar Litinin ne Sanchez ya koma Old Trafford a kuma ranar ya yi rubutu a shafinsa na Instagram cewae ''Na tuna ranar da na tattauna da Henry, dan wasa mai hazaka wanda ya sauya kungiya saboda dalili iri daya da muke da shi''.

Wannan batun ya sa wasu magoya bayan Arsenal ke fassara cewar Henry ne silar tafiyar Sanchez , sai dan dan kwallon Faransa ya ce bai ta ba cewa dan wasan Chile ya bar Gunners ba.

Sanchez ya ce Henry wanda ya koma Barcelona a 2007 yana kaunar Arsenal, inda ya yi rubuta a Twitter da cewar ''Zai yi kyau wata rana na ganshi yana horar da Arsenal''.

Labarai masu alaka