'Yan kwallo mafi tsada a City

Man City ta sayo Kevin de Bruyne daga Wolfsburg a kan kudi fam miliyan 55 a shekarar 2015. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Man City ta sayo Kevin de Bruyne daga Wolfsburg a kan kudi fam miliyan 55 a shekarar 2015.

Dan wasa mafi tsada a kungiyar Manchester City shi ne Kevin de Bruyne, wanda aka sayo daga Wolfsburg a kan kudi fam miliyan 55 a shekarar 2015.

Benjamin Mendy ne yake bi masa baya wanda aka sayo kan kudi fam miliyan 52 daga Monaco a shekarar 2017.

Sai kuma John Stones da aka dauko daga Everton a shekarar 2016 a kan kudi fam miliyan 47.5

Na hudunsu shi ne Kyle Walker wanda ya dawo kungiyar a kan kudi fam miliyan 45 a shekarar 2017.

Sai kuma na karshe Raheem Sterling wanda aka sayo daga Liverpool a shekarar 2015 akan kudi fam miliyan 44.

Yanzu kuma kungiyar na son daukar mai tsaron bayan Athletico Bilbao Aymeric Laporte a kan kudi fam miliyan 57 a matsayin dan kwallo mafi tsada a kulob din.

Labarai masu alaka