Sanchez ya bar kulob mai kayatarwa ya koma gagara-badau — Mourinho

A ranar Litinin ne Sanchez ya kom a United Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A ranar Litinin ne Sanchez ya kom a United

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce Alexis Sanchez ya bar kulob mai kayatarwa ya koma na gagara-badau, bayan da dan wasan ya bar Arsenal ya koma United.

Dan kasar Chilen ya koma Old Trafford a wata musaya da aka yi inda dan wasan tsakiya Henrikh Mkhitaryan ya koma Arsenal.

Mourinho ya ce "wannan yarjejeniya ta yi wa kowa dadi".

Ya kuma tabbatar da cewa Sanchez na cikin tagawar da za su fafata a gasar FA a Yeovil ranar Juma'a.

Saura kiris Sanchez, mai shekara 29, ya koma Manchester City a bazara, ya saka hannu a kan kwantiragin shekara hudu da rabi a United a kan fam miliyan 14 a shekara bayan an cire haraji.

Ya ci kwallo sau 80 a Aresnal bayan da ya koma kungiyar daga Barcelona a watan Yulin 2014, a kan fam miliyan 30, kuma shi ne wanda ya fi cin kwallo a kakar bara inda ya ci kwallo 30 a dukkaan wasannin da ya fafata.

"Mun samu daya daga cikin fitattun 'yan wasan da suka iya kai hari a duniya, kuma yana da matukar muhimmanci a wurinmu saboda muna bukatar gwarazan 'yan kwallo", in ji Mourinho.

Labarai masu alaka