Roger Federer ya lashe gasar Australian Open na shida

Roger Federer holds the Australian Open trophy Hakkin mallakar hoto Getty Images

Roger Federer ya lashe gasar Australian Open ta shida a rayuwarsa bayan ya lallasa Marin Cilic.

Wannan ne kuma gasar Grand Slam ta 20 da ya lashe a dukkan wasannin da ya shiga a tsawon rayuwarsa ta dan wasan Tennis.

Dan wasan wanda dan asalin kasar Suwizaland ne ya sami wannan nasarar ce bayan da a farko ya fara wasan da rashin sa'a, inda ya fadi a jerin sabis biyar a set na hudu.

Amma daga baya ya lashe wasan da 6-2 6-7 (5-7) 6-3 3-6 6-1.

Federer mai shekara 30 da haihuwa, ya kasance dan wasan Tennis na hudu a tarihin wasan da ya taba lashe gasar Grand Slam 20 ko fiye.

Wadanda suka sami wannan mukamin da ya samu a yau sun hada da Margaret Court, da Serena Williams da kuma Steffi Graf.

"Wannan ya kasance cikon burin da na dade ina rike da shi, kuma sai gaba daga nan," inji Federer.

Hanyar da Federer ya kai ga nasara

Wasanni Aboki wasa (mukami) Sakamako
Zagayen farko Aljaz Bedene 6-3 6-4 6-3
Zagaye na biyu Jan-Lennard Struff 6-4 6-4 7-6 (7-4)
Zagaye na uku Richard Gasquet (29) 6-2 7-5 6-4
Zagaye na hudu Marton Fucsovics 6-4 7-6 (7-3) 6-2
Zagayen kusa da na karshe Tomas Berdych (19) 7-6 (7-1) 6-3 6-4
Zagayen dab da kusa da na karshe Chung Hyeon 6-1 5-2 retired
Zagayen karshe Marin Cilic (6) 6-2 6-7 (5-7) 6-3 3-6 6-1

Labarai masu alaka