Ina jin dadin murza leda a PSG — Neymar

PSG Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption PSG ce ta daya a kan teburin gasar cin kofin Faransa

Dan kwallon tawagar Brazil, Neymar ya ce ya koma Paris St-Germain ne domin ya kafa tarihi, kuma yana jin dadin taka-leda a Faransa.

A labarin da jaridar Marca ta wallafa ta ce Neymar ya saba jin rade-radi a koda yaushe, saboda haka ba bakon abu bane a wajensa.

Dan kwallon ya kara da cewar duk lokacin da aka bude kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo sai an saka sunansa, babu abinda ba a ce a lokacin da yake Barcelona ba.

Neymar wanda ya koma PSG a matsayin mafi tsada a tarihi a bana, ya ci kwallo biyu a karawar da PSG ta doke Montpelier a gasar cin Kofin Faransa da suka buga a ranar Asabar.

A wasan ne Edison Cabani ya kafa tarihin dan wasan da yafi ci wa PSG kwallaye, sai dai Neymar ya ci gaba da buga wa kungiyar fenariti.

A baya can an samu takaddama kan wanda zai dunga buga wa PSG fenariti tsakanin Edison Cabani da Neymar.

Daga baya aka bukaci su sasanta a tsakaninsu, kuma hakan bai yi wu ba, har sai da kocin kungiyar ya bai wa Neymar alhakin buga fenariti a PSG.

Labarai masu alaka