'Yan Barcelona 18 da za su kara da Alaves

Barcelona Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Barcelona tana ta daya a kan teburin La Liga bayan wasa 20 da ta yi a gasar

Kocin Barcelona, Ernesto Valverde ya bayyana 'yan wasa 18 da za su kara da Deportivo Alaves a gasar La Liga a Camp Nou a ranar Lahadi.

A wasan farko da Barcelona ta ziyarci Alaves a kakar bana ta ci 2-0 a karawar da suka yi a ranar 26 ga watan Agustan 2017.

Sabbin 'yan wasan Barcelona, Philippe Coutinho da kuma Yerry Mina suna cikin 'yan kwallon da kocin ya bayyana.

Sai dai kuma Denis Suarez da Gerard Deulofeu suna cikin 'yan kwallon Barca da ke yin jinya da suka hada da Ousmane Dembele da kuma Thomas Vermaelen.

Ga jerin 'yan wasa 18 da za su fuskanci Alaves.

Ter Stegen, Semedo, Piqué, Rakitic, Sergio, Iniesta, Luis Suárez, Messi, Cillessen, Coutinho, Paulinho, Paco Alcácer, Jordi Alba, Digne, Sergi Roberto, Aleix Vidal, Umtiti and Yerry Mina.

Labarai masu alaka