Chelsea ta kai wasan gaba a kofin FA

Chelsea Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Chelsea tana ta uku a kan teburin gasar Premier bayan wasa 24

Chelsea ta kai zagaye na hudu a gasar cin Kofin FA, bayan da ta doke Newcastle United da ci 3-0 a karawar da suka yi a Stamford Bridge a ranar Lahadi.

Chelsea ta ci kwallo biyu ta hannun Michy Batshuayi a minti na 31 da kuma na 44, sannan Marcos Alonso ya ci na uku bayan da aka dawo daga hutu.

A makon jiya ne Arsenal ta fitar da Chelsea a gasar League Cup wasan daf da karshe.

Chelsea tana ta uku a kan teburin Premier da maki 50, bayan wasa 24 da ta kara a gasar.

A ranar Laraba Chelsea za ta karbi bakuncin Bournemouth a wasan mako na 25 a gasar ta Premier.

Labarai masu alaka