CHAN: Nigeria ta kai wasan daf da na karshe

CHAN 2018 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Nigeria za ta buga wasan daf da karshe da Sudan a ranar Laraba

Tawagar kwallon kafa ta Nigeria ta kai wasan daf da na karshe a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 'yan wasan da ke taka leda a nahiyar da ake yi a Morocco.

Nigeria ta kai wasan zagayen gaba ne, bayan da ta doke Angola da ci 2-1 a karawar da suka yi a ranar Lahadi.

Angola ce ta fara cin kwallo ta hannun Vladimir Etson Antonio Felix, bayan da aka koma daga hutun da kungiyoyin suka yi.

Super Eagles ta farke ta hannun Anthony Okpotu daf da za a tashi daga fafatawar.

Hakan ya sa aka tafi karin lokaci, inda Nigeria ta kara na biyu ta hannun Gabriel Okechukwu wanda hakan ya kai Super Eagles wasan daf da na karshe a gasar.

Nigeria za ta buga wasan daf da na karshe da Sudan a ranar Laraba a filin wasa na Marrakech.