Man City ta dauki Laporte mafi tsada a kungiyar

Man City Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Man City tana tra daya a kan teburin Premier ta kai wasan karshe a League Cup

Manchester City ta dauki dan kwallon tawagar Faransa mai tsaron baya, Aymeric Laporte daga Athletic Bilbao kan fam miliyan 57 a matsayin mafi tsada da ta saya a tarihi.

Laporte wanda har yanzu bai buga wa babbar tawagar Faransa tamaula ba, shi ne wanda aka dauka mafi tsada a Janairu, kuma kawo yanzu kungiyoyin Premier sun kashe fam miliyan 252 wajen daukar 'yan kwallo a watan.

Bayan da City ta sayi Laporte mai shekara 23, Pep Guardiola ya kashe kudi fam miliyan 215.5 wajen daukar masu tsaron baya da mai tsaron raga tun daga karshen kakar bara.

Dan kwallon da City ta saya mafi tsada a tarihi a baya shi ne Kevin de Bryne kan fam miliyan 55 a shekara 2015.

Laporte mai tsaron baya daga tsakiya ya buga wa matasan tawagar Faransa 'yan 21 wasa 19.

Labarai masu alaka