Ahmed Musa ya koma CSKA Moscow

CSKA Moscow Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ahmed Musa ya ci kwallo uku a wasa 33 da ya buga wa Leicester City

Dan wasan Leicester City, Ahmed Musa ya sake komawa CSKA Moscow domin ya buga mata wasanni aro zuwa karshen kakar shekarar nan.

Dan wasan tawagar kwallon kafar Nigeria, mai shekara 25 ya koma Leicester City daga CSKA kan yarjejeniyar shekara hudu kan fam miliyan 16 a matsayin wanda aka saya mafi tsada a kungiyar a Julin 2016.

Sai dai dan wasan ya kasa tabuka abin azo a gani tun lokacin da ya koma Ingila da murza-leda, inda ya ci kwallo uku a wasa 33 da ya buga wa Leicester City.

CSKA ta ce za ta saka sunan Musa a cikin 'yan wasan da za su buga mata gasar cin Kofin Europa a karawar da za ta yi nan gaba.