Sanchez zai buga wa United Premier ranar Laraba

Man United Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Manchester United tana ta biyu a kan teburin Premier

Ana sa ran Alexis Sanchez zai buga wa Manchester United wasan Premier na farko a karawar da za ta yi da Tottenham a Wembley a ranar Laraba.

Dan wasan tawagar kwallon kafa ta Chile ya buga wa United wasan zagaye na hudu a kofin FA da ta doke Yeovil a ranar Juma'a tun komawar sa daga Arsenal.

Babu wasu 'yan wasan da suka ji sabon rauni a United, hakan na nufin Zlatan Ibrahimovic da kuma Eric Bailly ne suke yin jinya har yanzu.

'Yan wasan da ake sa ran za su buga wasan United:

De Gea da Romero da Young da Jones da Smalling da Lindelof da Valencia da Shaw da Rojo da Darmian da Matic da Pogba da kuma, Blind.

Sauran sun hada da Fellaini da Carrick da Herrera da McTominay da Martial da Rashford da Lingard da Mata da Sanchez da kuma Lukaku.

Labarai masu alaka