Pillars ta hada maki uku a kan Plateau United

Nigerian Premier League Hakkin mallakar hoto NPFL Twitter
Image caption Kano Pillars tana ta uku a kan teburi da maki 11, bayan da ta buga wasa 6

Kano Pillars ta yi nasarar cin Plateau United 2-0 a gasar cin Kofin Firimiyar Nigeria wasan mako na shida da suka kara a ranar Laraba.

Pillars ta ci kwallayen ta hannun Lokosa a minti na 21 da fara wasa, sannan minti shida tsakani ya kara na biyu a fafatawar da suka yi a filin wasa na Sani Abacha da ke kofar Mata a Kano.

Da wannan sakamakon Kano Pillars tana ta uku da maki 11 a kan teburi, ita kuwa Plateau United tana ta biyu da maki 12, Akwa United ce ta daya da maki 13.

Ga sakamakon wasannin mako na shida da aka yi:

  • FC IfeanyiUbah 1-1 Akwa United
  • Yobe Desert Stars 1-0 Katsina United
  • Enyimba 1-0 Abia Warriors
  • Sunshine Stars 1-0 El-Kanemi Warriors
  • MFM 2-1 Wikki Tourist