Chelsea ta dauki Olivier Giroud

Chelsea Hakkin mallakar hoto ChelseaFC
Image caption Giroud ya buga wa Arsenal wasa 253 ya kuma ci kwallo 105

Chelsea ta dauki Olivier Giroud daga Arsenal kan yarjejeniyar wata 18, kan kudi fam miliyan 18.

Giroud dan kwallon tawagar Faransa, mai shekara 31, ya bar Arsenal wadda ya yi wa wasa 253 ya ci kwallo 105 tun komawarsa Emirates daga Montpellier kan fam miliyan 12 a Yunin 2012.

Borussia Dortmund ta tabbatar da daukar aron dan wasan Chelsea, Michy Batshuayi wanda zai yi mata wasanni zuwa karshen kakar bana.

Tun farko Arsenal ce ta dauki Pierre-Emerick Aubameyang daga Dortmund wadda ta ce sai ta samu wanda zai maye gurbin Aubameyang kafin ya bar Jamus.

Arsenal ta dauki dan kwallon tawagar Gabon ne, domin ya maye gurbin Alexis Sanchez wanda ya koma Manchester United da taka-leda.

Labarai masu alaka