Wa zai lashe kofin CHAN, Nigeria ko Morocco ?

Chan 2018 Hakkin mallakar hoto Caf
Image caption Nigeria da Moroccio babu wadda ta taba lashe kofin CHAN

Tawagar kwallon kafa ta Nigeria za ta fafata da ta Morocco a wasan karshe a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta yan wasan da ke murza leda a nahiyar da ake kira CHAN.

Super Eagles ta kai wasan karshe ne bayan da ta ci Sudan 1-0 a wasan daf da karshe da ta buga a ranar Laraba.

Nigeria ta karasa wasan da 'yan was 10 bayan da aka korar mata Ifeanyi Samuel Nweke, ita ma Sudan an bai wa Bakri Basheer jan kati.

Ita kuwa Morocco cin Libya 3-1 ta yi, bayan da kara musu lokaci, kuma tun farko 1-1 da suka tashi.

Wannan ne karon farko da kungiyoyin biyu za su buga wasan karshe a gasar da ake yi karo na biyar.

Yadda Morocco ba ta taba daukar kofin ba, haka ma Nigeria, wadda ta taba yin ta uku a 2014 a jagorancin Stephen Keshi.

Jamhuriyar Congo tana da kufin guda biyu sai Libya da Tunisia da kowacce ta dauka sau dai-dai.

Super Eagles da Morocco sun buga wasa biyar a gasar bana, inda Nigeria ta ci kwallo bakawi, ita kuwa Morocco 11 ta ci, kuma guda bibiyu suka shiga ragar kowacce.

Labarai masu alaka