Everton ta dauki aron Mangala

Mangala na cikin tawagar Faransa a gasar cin kofin duniya ta 2014 amma bai buga kowanne wasa ba Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mangala na cikin tawagar Faransa a gasar cin kofin duniya ta 2014 amma bai buga kowanne wasa ba

Everton ta dauki aron dan kwallon Manchester City Eliaquim Mangala har zuwa karshen kakar bana, inda zai fafata a gasar wasannin Firimiya.

Dan kasar Faransan mai shekara 26 shi ne na uku da kungiyar ta dauka a kasuwar 'yan tamaulan da aka bude ta watan Janairu, bayan Theo Walcott and Cenk Tosun.

Mangala ya koma City daga Porto a shekarar 2014 akan fam miliyan 32, kuma wasa hudu kawai ya buga a gasar Firimiyar bana.

Ya bar kulob din bayan da City ta dauki Aymeric Laporte daga Athletic Bilbao a kan fam miliyan 57.

Mangala ya yi wa City wasa sau 79 tun bayan da ya koma kungiyar daga Portugal, sai dai ya kusan shafe kakar 2016-17 a Valencia yana taka-leda a matsayin aro.

Labarai masu alaka