Tottenham ta dauki Lucas Moura

Lucas sai saka riga lamba 27 a Tottenham Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Lucas sai saka riga lamba 27 a Tottenham

Tottenham ta dauki dan kwallon Paris St-Germain Lucas Moura a kan fam miliyan 23.

Dan wasan dan Brazil mai shekara 25, ya saka hannu a kwantiragin har zuwa 2023, ya koma PSG akan fam miliyan 33.5 daga Sao Paulo a shekarar 2013, sai dai wasa shida kawai ya buga a bana.

Moura ya ce, "Zan yi iya kokarina a wannan kulob din saboda ina ganin muna da kwarewa da dama kuma zamu iya samun nasara a manyan wasanni."

Ya kara da cewa,"Na yi matukar farin ciki, saboda babban kulob ne kuma ina fata zan ji dadin zama a ciki, zan yi aiki tukuru da kuma nuna kwarewata".

Lucas zai saka riga lamba 27 a Tottenham, ya ci kwallo 46 ya kuma taimaka an ci sau 50 a karawa 229 da ya yi a kungiyar ta Faransa.

Labarai masu alaka