West Ham ta dakatar da Tony Henry

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption West Ham ta ce ba zasu amince da duk wani abu da ya shafi nuna wariya ba.

West Ham ta dakatar da daraktan daukar 'yan kwallo Tony Henry bisa ikirarin da ya yi na cewa kungiyar ba za ta sake daukar 'yan wasan Afirka ba.

Jaridar Daily Mail ta bayar da rahoton cewa Henry ya ce,'yan kwallon Afirka na haddasa gutsiri-tsoma, "idan ba sa cikin kungiya".

A bayanin, West Ham ta ce ba za ta amince da duk wani abu da ya shafi nuna wariya ba.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta ce zata gudanar da bincike a hukumance kan lamarin.

Kungiyar na da 'yan wasa 'yan Afirka shida, wadanda suka hada da Cheikhou Kouyate, da Pedro Obiang, da Joao Mario, da Angelo Ogbonna, da Arthur Masuaku da kuma Edimilson Fernandes.

Dan kwallon Senegal Diafra Sakho ya bar kungiyar a kasuwar 'yan tamaulan watan Janairu, inda ya koma Rennes, da kuma na Ghana Andre Ayew wanda ya koma Swansea.

Labarai masu alaka